Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawarsa da gidan radiyon Sputnik kan zaman gaggawa da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa suka kira a jiya Laraba da kuma wanda zasu gudanar a nan gaba, tsohon jami'in jakadancin kasar Masar ya bayyana cewa, Babu wani abin da zaman zai haifar illa yin tofin Allah tsine kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Haka nan kuma ya kara da cewa, Tun a lokacin da shugaban kasar Amurka ya shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila ya dace kungiyar kasashen Larabawa su dauki matakin kalubalantarsa amma a halin yanzu da lokaci ya kure musu babu wani tasirin da zasu yi kan matsalar.