IQNA

Bude Iyakokin Mauritania Da Aljeriya

23:43 - August 04, 2018
Lambar Labari: 3482860
Bangaren kasa da kasa, Mahukuntan kasar Mauritania sun sanar da cewa, ana shirin sake bude mashigar Tanduf da ke kan iyaka tsakanin kasar da kuma Aljeriya nan ba da jimawa ba.

Kamfanin dillancin labaran qna ya habarta cewa,

gwamnatocin mauritania da kuma Aljeriya sun cimma matsaya kan sake bude mashigar Tanduf a cikin 'yan makonni masu zuwa, domin ci gaba da zirga-zirgar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta wannan mashiga.

Bayanin ya ce wannan mashiga tana da matukar muhimmanci ga kasashen biyu, domin ta hanyar yin amfani da ta za a samu suki shigar da kaya da kuma fitar da su tsakanin Aljeriya da Mauritania da ma sauran kasashen yammacin Afrika.

Yanzu haka kasashen biyu sun fara aiki na hadin gwiwa domin gaggauta dawo aikin shige da fice a wannan mashiga kamar yadda aka saba a wasu shekaru da suka gabata.

3735800

 

captcha