Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Kofi Annan ya rasu yau Asabar a wani asibiti da ke birnin Bern na kasar Switzerland yana da shekaru 80 a duniya.
Kofi Annan wanda ya yi aiki tsawon shekaru a majalisar dinkin duniya, ya zama babban sakataren majalisar a tsakanin shekarun 1997 zuwa 2006.
Ya zama babban manzon majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria, daga bisani ya yi murabus sakaakon matsin lamabar da ya yi ta fuskanta domin ya murguda gaskiyar abin da yake faruwa a kasar. Haka nan kuam ya zama babban manzon majalisar mai sanya ido kan halin da 'yan kabilar Rohingya suke ciki bayan kisan da aka yi musu a Myanmar.
Sakamakon ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya da Kofi Annan ya yia duniya, ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.