IQNA

Sabbin Kwasa-kwasai A jami’ar Musulunci Ta Ghana

23:30 - September 30, 2018
Lambar Labari: 3483021
Bangaren kasa da kasa, Babbar jami’ar musulunci ta kasar Ghana ta bullo da wasu sabbin kwasa-kwasai da za a rika koyarwaa cikinta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bisa sanarwar da ofishin babban jami’i mai kula da tsare-tsare na jami’ar ya bayar, daga cikin sabin kwasa-kwasan akwai koyar da ilimin tarbiyya da kuma ilimin zamantakewar al’ummomi.

Jami’ar muslunci ta kasar Ghana dai tana daga cikin jami’oin da suke samun karbuwa a tsakanin al’ummar kasar har ma da wasu daga cikin al’ummomin kasashen Afirka ta yamma.

Wannan jami’a dai tana kokarin ganin ta koyar da ilmomi da suka danganci muslunci a zamanance, kamar yadda kuma take koyar da wasu ilmomin daidai da sauran jami’oi domin tsarinta ya tafi bai daya a wasu bangarorin da sauran jami’oin kasar a hukumance.

Kasar Ghana dai tana daya daga cikin kasashe masu tasiri a yankin yammacin nahiyar Afirka ta fuskoki da dama, da suka hada hard a bangaren ilimi.

 

3751330

 

 

 

 

captcha