IQNA

Masar Ta Dawo Wani Tsohon Kwafin Kur’ani

23:40 - October 19, 2018
Lambar Labari: 3483056
Bangaren kasa da kasa, Masar ta samu nasarar dawo da wani tsohon kwafin kur’ani mai tsarki bayan fitar da shi daga kasar na tsawon shekaru.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habart cewa, gwamnatin kasar ta Masar ta ta samu nasarar dawo da tsohon kwafin kur’anin ne mai rubutu da ake ake kira Atlas Susman Saidid, bayan fitar da shi daga kasar na tsawon shekaru zuwa kasar Jamus.

An dawo da wannan kafin kur’anin ne bayan da mutumin da yake mallakarsa a kasar ta Jamus ya fitar da shi domin sayarwa, inda ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar Msar ta gagauta domin fansarsa.

Wannan kwafin kur’ani an fanshe shi ne akan kudi yuro dubu ashirin da shida, kuma yanzu haka an dawo da shi kasar Masar, tare da hadin gwiwa da gwamnatin Jamus.

3757053

 

 

 

captcha