Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, sahayoniyar sun riya cewa matashin Bapalasdinan ya yi kokarin sarin wani soja ne da wuka.
Sau da yawa sojojin Sahayoniya suke harbe Palasdinawa suna masu riya cewa za su kai hari da wukake akan sojoji ko 'yan share wuri zauna.
Wani labarin daga Palasdinu ya ambaci cewa; Sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hari akan Palasdinawa a mashigar Kalandiya.
A kowace rana ta Allah, 'yan sahayoniya suna kai hari ko kuma kama Palasdinawa a yankunan daban-daban na yammacin kogin Jordan.