IQNA

Sojojin Najeriya Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Shi’a

23:41 - October 30, 2018
Lambar Labari: 3483083
Bangaren kasa da kasa, Sojojin gwamnatin Najeriya sun bude wuta akan mabiya mazhbar Shi'a da ke tattakin arba'in a kusa da birnin tarayya Abuja.

Kamfanin dillancin labarun euro news ya ambato cewa daruruwan 'yan shi'ar kasar sun gudananr da Zanga-zanga suna masu yin kira da a saki jagoransu na harka Islamiyya.

A jiya an ambaci cewa adadin wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar kisan da sojojin su ka yi musu a yankin Cujo ya kai sha shida yayin da wasu masu yawa su ka jikkata.

Tun a ranar 13 ga watan Disamba na 2015 ne aka kame shekih zakzaky tare da mai dakinsa malama Zinat, bayan kisan gillar da aka yi wa daruruwan mabiyansa a birnin Zaria.

A shekaran jiya Lahadi ma an sami wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar bude musu wuta da sojoji su ka yi a yankin Zuba.

3759948

 

 

 

 

 

 

captcha