Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin jaridar Al-shuruq ta kasar Tunisia ya bayar da rahoton cewa, sakamakon kararrakin da kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkokin falastinawa a kasar Tunisia, domin hana tawagar Isra'ila halartar wani taron addinai da za a gudanar a kasar, kotun ta yanke hukuncinta na karshe, inda ta haramta shigowar tawagar Isra'ila a cikin kasar domin halartar taron.
Kungiyoyin sun dauki wannan matakin ne domin nuna rashin amincewarsu da abin da Isra'ila take na kisan gilla a kan al'ummar Falastinu, ba tare da duniya ta damu da hakan ba, yayin da kuma a lokaci guda ma wasu daga cikin kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya, suke ta hankoron ganin sun kulla alaka da Isra'ila.
A ranar 8 ga wannan wata na Nuwamba ne za a fara gudanar da taron mabiya addinai na duniya a birnin Tunis na kasar Tunisia, wanda zai samu halartar wakilai daga kasashen duniya daban-daban.