Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da wani gagarumin taron maulidin manzon Allah (SAW) a garin qirawan na kasar Tunisia, daya daga cikin garurwa masu tarihi a addinin muslunci.
Wannan taron maulidi na dya daga cikin irinsa da ake gudanar a dukkanin biranan kasar ta Tunisia, wanda bisa ga al'ada akan fara tarukan ne daga lokacin da watan an maulidi ya shigo.
Ma'ikatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar na bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin an gudanar da tarukan na maulidin manzon (SAW) a birane da kauyuka.
Malaman addinin muslucni sukan gabar da jawabai kan tarihin manzon Allah (SAW) da kuma irin darussan da suke kunshe a cikin rayuwar tasa mai albarka, wanda dukkanin mutane musulmi da ma wadanda ba musulmi ba za su iya yin koyi da su a cikin rayuwa.