IQNA

Ana Ci Gaba Da Tarukan Maulidin Manzon Allah A Kasashen Musulmi

20:15 - November 22, 2018
Lambar Labari: 3483142
Ana ci gaba da gudanar da tarukan maulidin manzon Allah a kasashen musulmi daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tun daga ranar 12 ga watan Rabiul Awwal musulmia  ko'ina  acikin fadin duniya suke gaba da gudanar da tarukan murnar zagayowar lokacin maulidin manzon Allah (SAW).

Rahotanni daga kasashen duniya musamman na musulmi sun nuan cewa, a wannan shekara yadda ake gudanar da maulidi a duniya ya sha banban da sauran shekaru, inda  a wannan lokaci lamarin ya kara bunkasa fiye da sauran shekarun da suka gabata.

A mafi yawan wuraren tarukan murnar maulidin manzon Allaha  kasashen duniya, ana gudanar da taruka ne, inda malama suke gabatar da jawabai na tunatar da al'ummar musulmi matsayin manzon Allah da kuma irin kyawawan halayensa, da yadda ya kamata musulmi su zama masu koyi da shia  cikin lamarinsu.

Baya ga haka kuma, a wasu kasashen ma har a kan gayyaci wasu mabiya addinai zuwa wadannan taruka, domin su kara samun masaniya kan manzon Allah da kuma addininsa mai tsarki.

A kasashen turai da da dama muuslmi suna ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka, kamar yadda haka lamarin yake a kasashen Afrika da dama da kuma kasashen nahiyar Asia da kuma da dama daga cikin kasashen larabawa.

3766275

 

 

captcha