IQNA

Gwamnatin Masar ta Hana Yada bayanin Azhar Kan Batun Gado

18:46 - November 27, 2018
Lambar Labari: 3483156
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Masar ta hana kafofin yada labarai yada wani bayani da Azhar ta fitar kan batun daidaita gado tsakanin mata da maza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu 'yan jarida sun sanar da cewa, a jiya an umarce da kada su yada wani bayani da Azhar ta fitar kan batun daidaita gado tsakanin mata da maza a mahanga ta shari'a.

Wannan mataki na gwamnatin kasar Masar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin take-taken gwamnatin kasar na nuna goyon baya ga masu ra'ayin cewa gado tsakanin mace da namiji duk abu daya ne babu wani banbanci, abin da namiji zai samu shi ne mace za ta samu.

Cibiyar Azhar ta fitar da wani bayani domin mayar da martani ga Sa'ad Al-hilali daya daga cikin malaman cibiyar, wanda ya fitar da wani bayani da ke cewa, a shar'ance ya halasta a raba gado daidai tsakanin mace da namiji.

Azhar ta bayyana wanann bayani da cewa yin shishigi a cikin umarnin Allah, domin kuwa batun gado Allah ya raba shi da kansa filla-filla a cikin kur'ani mai tsarki, kuma duk wani bayanin sabanin abin da ya ambata  acikin kur'ani, to ba ya da wata kima a shar'ance.

Yanzu haka dai wannan bayani na ci gaba da fuskantar martani daga bangarori daban-daban na malamai da masana a ciki da wajen kasar ta Masar.

3767318

 

 

captcha