Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ahmad Taufiq ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai masallai kimanin 1000 da suke bukatar gyara na hakika a cikin kasar morocco.
Ministan ya ci gaba da cewa, bangarenb gwamnati da kuma kungiyoyin da suke bayar da tallafi domin gudanar da ayyukan alkhari duk suna yin iyakar kokarinsu a wannan fage.
Ya kara da cewa, a halin yanzu akwai wasu masallatai da aka gina da adadin ya kai 185, kuma 150 daga cikinsu duk kungiyoyi masu gudanar da ayyukan alkhairi ne suka gina su, wanda a cewarsa wannan babban ci gaba ne.