IQNA

Amnesty Int. Ta Soki Kasar Bahrain Kan Muzgunawa ‘yan adawar Sisyasa

16:01 - December 02, 2018
Lambar Labari: 3483174
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adam ta kasa da kasa Amnesty International ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan janye hakkin zama dan kasa ga mutane 32 a Bahrain.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Manama Post ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da kungiyar ta Amnesty International ta fitar, ta bayyana janye hakkin zama dan kasa da gwamnatin Bahrain take yia kan ‘yan adawar siyasa da cewa babban cin zarafin dan adam ne.

Bayanin ya ce irin salon mulkin kama karya da masaratar Bahrain take bi yay i hannun riga da dukkanin dokoki na siyasa a duniya, domin kuwa ana korar mutum daga kasarsa bayan cin zarafinsa, saboda ya bayyana ra’ayinsa na siyasa.

A ranar Alahamis da ta gabata, masarautar Bahrain ta janye hakkin zama dan kasa daga mutane 32 saboda mahangarsu ta siyasa wadda ta sabawa gwamnati, a cikin wanann shekara da muke ciki, masarautar Bahrain ta kwace hakkin zama dan kasa daga mutane 288 dukkaninsu ‘yan kasar Bahrain ne saboda dalilai na siyasa.

Daga shekara ta 2012 ya zuwa yanzu, adadin mutanen da aka kwacewa hakkinsu nazama ‘yan kasa a Bahrain saboda dalilai na siyasa da bangaranci na akida, ya kai mutane 794.

3768282

captcha