IQNA

Manzon MDD Ya Isa Birnin San'a Na Yemen

23:59 - December 23, 2018
Lambar Labari: 3483246
Bangaren kasa da kasa, Jagoran tawagar masu sanya ido na MDD kan rikicin Yemen ya isa Sanaa babban birnin kasar ta Yemen da 'yan Houtsie ke rikeda, bayan da ya ziyarci birnin Aden a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Janar Patrick Cammaert, zai yada zango a birnin na Sanaa, kafin ya wuce Hodeida kamar yadda wata majiyar MDD ta sanar, saidai ba tare da yin karin bayyani ba ko zai isa yammacin kasar dake karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ko baya ga jagoran tawagar akwai wasu jami'an na MDD masu sanya ido su guda shiga da suka isa birnin na Sanaa.

A birnin Aden inda ya fara isa a jiya Asabar, jagoran tawagar masu sanya ido, ya bukaci dukkan bangarorin dake rikici da juna a kasar ta Yemen dasu mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Hodeida, sannan su bada hadin kai domin samun damar isar da kayan agaji daga Hodeida zuwa cikin sauren sassan kasar, kamar yadda kakakin sakatare na MDD, Stéphane Dujarric, ya sanar a cikin wata sanarwa.

A ranar 26 ga watan nan ne ake sa ran za'a gudanar da taron farko na kwamitin bangarorin dake rikici na Yemen. 

 

3774902

 

 

captcha