IQNA

‘Yan Majalisar Amurka Musulmi Suna Goyon Bayan Haramta Kayan Isra’ila

21:48 - February 10, 2019
Lambar Labari: 3483360
Bangaren kasa da kasa, Ilhan Umar da Rashida Tlaib ‘yan majalisar dokokin Amurka musulmi biyu sun nuna goyon bayansu ga duk wani mataki na haramta kayan Isra’ila a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan mataki da wadannan ‘yan majalisar dokokin Amurka biyu suka dauka ya bakanta ran Isra’ila matuka.

Baya ga haka kuma wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka sun nuna damuwa matuka dangane da yadda wadannan ‘yan majalisar suka nuna matsayinsu na kiyayya da Isra’ila a fili.

A lokacin da suke bayani sun bayyana cewa, dukkanin matsalolin da ake fuskanta tsakanin yahudawa da Palastinawa gwamnatin Isra’ila ce ta hadda su.

Kungiyar haramta kayan Isra’ila BDS dai wasu Falastinawa da kuma masu fafutuka a duniya  suka kafa ta, kuma kungiyar tana yin kira ne da a kaurace wa dukkanin kayan da Isra’aila take samarwa, domin kuwa ita gwamnati ce ta wariya kamar irin gwamnatin wariya da aka yia  kasar Afrika ta kudu.

3789082

 

 

 

captcha