IQNA

Ahmad Azum: Gwamnatin Tunisia Za Ta Ci Gaba kare Makarantun Kur’ani

23:44 - February 22, 2019
Lambar Labari: 3483396
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin addini a kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da kare makarantun kur’ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ya yi da tashar shams FM a jiya, minister mai kula harkokin addini a kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin ganin ta inganta  makarantun kur’ani a kasar.

Yace ko shakka babu ma’ikatarsa ta gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci a cikin lokutan baya-bayan nan, da hakan ya hada da gina makarantun kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma ya yi ishara da ginin sabuwar makarantar kur’ani ta Ibn Umar da ke yankin Alriqab a cikin gundumar Buziz, inda ya ce wannan na daga cikin muhimman ayyukan da suka sanya  agaba a halin yanzu.

Furucin na ministan kula da harkokin addini na Tunisia ya zo ne bayan kakkausar sukar da ya sha daga bangarori daban-daban na al’ummar kasar, bayan da ya yi dirar mikiy a kan makarantun kur’ani a baya.

3792312

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha