IQNA

Martanin Ayatollah Isa Kasim Kan Taron Kimiyya Da Fasaha Na Bahrain

23:34 - April 03, 2019
Lambar Labari: 3483512
Babban malamin addinin mulsunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya mayar da kakakusan martani kan gayyatar Isra'ila a taron kimiyya da fasaha da za agudanar a kasar Bahrain.

kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Lualuatv ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar da jiya, Babban malamin addinin mulsunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim wanda a halin yanzu yake zaune a birnin Qom na kasar Iran, ya mayar da kakakusan martani kan gayyatar Isra'ila a taron kimiyya da fasaha da za  agudanar a kasar Bahrain a cikin makonni biyu masu zuwa.

Shehin malamin ya ce babban abin kunya ne ga sarakunan larabawa da wasu shugabanninsu, yadda suke ta hankoron ganin sun kusantar da kansu ga yahudawan sahyuniya  tare da biya musu bukatunsu.

ya ce gayyatar Isra'ila a wurin taron da za a gudanar a Bahrain kan harkokin kimiyya da fasaha cin amana ne ga al'ummar Palastine, da sauran al'ummar musulmi ta duniya.

A cikin makonni biyu masu ne dai za a gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin kimiyya da fasaha  akasar bahrain, wanda gwamnatin kasar ta shirya, kuma ta gayyaci jami'an gwamnatin Isra'ila zuwa taron, daga cikinsu ahr da ministan harkokin tattalin arzikin Isra'ila Illy Kohen, tare da wasu jami'an Isra'ila kimanin 45 da za su rufa masa baya.

3800742

 

captcha