Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto rahoto daga reuters cewa, majalisar sojoji da ke tafiyar da mulki a kasar Sudan ta kasa shawo kan ‘yan adawa domin samu daidaito kan batun mika mulki.
Majalisar sojojin ta bayyana ci gaba da gudanar da zanga-zanga da gangami da ‘yan adawa suke yi da cewa ba zai taimaka ba wajen warware matsalar da kasar ta samu kanta a ciki.
Bayanin majalisar sojin ya yi nuni da cewa; akwai bukatar a zauna a fahimci juna tsakanin majalisar sojin da kuma sauran dukkanin bangarori na siyasa da na al’umma, domin samun daidaiton baki kan yadda za a mika mulki ga farar hula, da kuma hanyoyin da za a bi kafin kaiwa ga hakan.
Sai dai a nasu bangaren bangarorin adawa sun yi watsi da wannan kira, inda suke jaddada bukatar su ga sojojin das u mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta farar hula, wadda za ta shirya sahihin zabe na dimukradiyya a kasar.