IQNA

Jagora: Yunkurin Amurka Na hana Sayar da Man Iran Zai Fuskanci martani

20:14 - April 25, 2019
Lambar Labari: 3483575
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, matakin da Amurka ta dauka na hana sayen mai daga Iran ba zai taba wucewa ba tare da martani ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah ya tabbatar da cewa kiyayyar daHukumomin Amurka ke yiwa al'ummar Iran domin mika wuya ta hanyar matsin lambar tattalin arziki, har abada ba za su mika wuya, kuma su sani cewa bayan amfani da lokaci na samar da ayyukan ci gaba, wannan kiyayya da makarkashiya ba za ta kasance ba tare an mayar da martani ba.

A yayin da yake ganawa da duban ma'aikata albarkacin jagoyowar makon ma'aikata, a wannan Laraba Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kokarin da Amurka ke yi na toshe hanyoyin sayar da man fetir din kasar ba zai ci nasara ba, kuma duk yawan man fetir din da kasar Iran ke son sayarwa a Duniya za ta sayar.

Yayin da yake jan hankalin makiyan al'ummar kasar Iran, jagora ya tabbatar da cewa ku sani cewa wannan kiyayya ta ku ba za fice ba tare da an mayar muku da martani ba, kuma ku san cewa Al'ummar Iran ba al'umma ba ce da za a kulla mata makirci, ta zauna tana kallo ba.

A yayin da ya koma kan batun tsananin matsin da Amurka ke yi na sayan man fetir din kasar, Jagoran juyin juya halin musulunci ya ce rage sayar da man fetir, a wajenmu wata dama ce na kara dogaro da karfinmu na cikin gida.

Har ila yau jagora yayin da yake ishara kan da'awar hukumomin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila ya ce suna fadar cewa suna kiyayya ne da tsarin musulinci ba wai al'ummar kasar Iran ba, kiyayya da tsarin musulinci, kiyayya ne ga Al'ummar kasar Iran, domin da taimakon al'ummar Iran aka shinfida tsarin musulinci, idan ba da taimakon al'ummar Iran ba, da tsarin musulinci ba tabbata a kasar Iran ba.

3806125

 

 

 

 

captcha