IQNA

Shugaban kawamitin Siyasar wajen majalisar Iran ya yi Bayani kan furicin zarif

15:01 - April 28, 2019
Lambar Labari: 3483585
Bangaren siyasa, shugaban kwamitin kula da harkokin siyasar waje a majalisar dokokin kasar Iran ya yi Karin haske kan furucin Zarif.

Heshmatollah Fallahat Pishe shugaban kwamitin kula da harkokin siyasar waje a majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, furucin da ministan harkokin wajen Iran ya yi kan shawarar day a kawo akn tattaunawa da Amurka domin musayar fursunoni magana ce da ke kan hanya.

Ya ce a kowane lokaci bababn aikin ma’;aikatar waje shi ne kokarin kwakwafa lamurra na diflomasiyya da kuam gyara su, wanda kuma bisa masaniya da ilimi ne zarif ya fadi hakan, amma kuma lokaci guda hakan ba yana nufin ana gudanar da wata tatatunawa ne tsakanin Amurka da Iran ba.

Ya ce a kowane lokaci kasar Iran tana son zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakaninta da kasashe, kuma bisa wannan siyasar take tafiyar da lamurranta, amma Amurka wadda take son ta mayar da kowa bawanta ko Karen farautarta, ba za ta amince da haka ba, domin kuwa Iran kasa ce wadda ked a siyasa mai ‘yanci.

Haka nan kuma ya bayyana matsayar da Amurka ta dauka da cewa babban kure ne na siyasa, domin yin fito na fito da Iran ba maslaha ce ga Amurka a ba, hatta ‘yan koren Amurka da ke kare manufofinta yankin gabas ta tsakiya, ba mashalarsu ce a yi irin wannan fito na fito ba.

3806754

 

captcha