IQNA

An Shiga Tattaunawa Tsakanin ‘yan Adawa Da Sojoji A Sudan

23:35 - April 29, 2019
Lambar Labari: 3483588
A Sudan jagororin masu zanga zanga, da sojojin dake rike da mulki sun koma bakin tattaunawa yau Litini, domin kafa wata majalisar hadin gwiwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Ansarullah ya habarta cewa, a wani lokaci nan gaba ne ake sa ran bangarorin zasu fitar da wata sanarwa ta bai daya, inda za a kafa majalisar gwamnatin rikon kwarya wadda za ta hada sojoji 7 da kuma farar hula 8 a matsayin mambobi.

Tattaunawar da bangarorin keyi na zuwa ne kwana biyu bayan sanarwar da suka fitar ta cimma matsaya ta kafa wata hukuma data kunshi sojoji da kuma fararen hula.

Yarjejeniyar dai ta amince da bukatun masu zanga zanga, dake ci gaba da zaman dirshin gaban hedikwatar sojin kasar, makwanni biyu bayan hambarar da gwmanatin shugaba Umar Hassan Albashir.

Ana sa ran majalisar kolin da za’a kafa wacce ta kumshi sojoji da kuma fararen hula, zata kafa gwamantin wucin gadi ta fara hula, wacce kuma zata tafitar da al’amuran kasar da kuam shirya zabubuwan farko tun bayan kifar da mulkin shugaba Albashir da ya kwashe shekaru talatin yan mulkin kasar.

3807381

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha