IQNA

Dalibai Bakaken Fata Musulmi sun Gudanar da Taro A Amurka

23:48 - May 01, 2019
Lambar Labari: 3483594
Daliban jami’a musulmi bakaken fata a kasar Amurka, sun gudanar da wani zaman taro na farkoajami’ar birnin New York.

Shafin yada labarain na Middle East ya bayar da rahoton cewa, ajiya daliban jami’a musulmi bakaken fata ‘yan kasar Amurka, sun gudanar da wani zaman taro na farkoajami’ar birnin New York karkashin kungiyar Balac Muslim Initiative.

Babbar manufar taron dai ita ce yin dubi bisa ga irin gagarumar rawar da musulmi babkaken fata suka takaa kasar ta Amurka wajen yada musulunci a tsakanin al’ummar kasar.

Wasu daga cikin manyan malaman jami’a da masana bakaken fata musulmi na kasar Amurka sun halarci wurin taron, kamar yadda dalibai da dama akasarinsu bakaken fata ne musulmi har da wasu wadanda ba musulmi ba sun halarci taron.

Wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai sun yi ishara da irin rawar da wasu daga cikin fitattun bakaken fata musulmi suka taka a kasar, wajen kare hakkokin bakaken fta da kuma al’ummomi marassa rinjaye akasar a cikin tarihi.

Haka ann kuma wasu sun bayyana dalilan da suka sanya aka samu musulmi da dama a cikin bakaken fata na kasar Amurka, wnada hakan ya hada da kwaso wasu bakaken fata musulmi domin bautar da su daga wasu kasashen Afrika, musamman daga kasashen Gambia, Senegal da ma kasar Kamaru.

 

3807707

 

 

 

 

captcha