IQNA

Sabani Tsakanin Rasha Da Amurka Ya Kara Bayyana A Fili

23:59 - May 15, 2019
Lambar Labari: 3483644
A ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo yake gudanarwa a kasar Rasha, irin sabani da baraka da ke tsakanin kasashen biyu sun kara bayyana a fili.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya isa birnin Sochi na kasar Rasha, inda ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov.

A yayin taron manema labarai da suka gudanar bayan kammala tattaunawarsu, baraka da wagegen gibin da ke akwai a mahangar kasashen biyu kan lamurra da dama na duniya, sun kara bayyana.

Dukkanin bangarorin biyu ba su boye sabani da suke da shi kan lamurra na kasa da kasa ba, inda ministan harkokin wajen Rasha ya ce, sun tattauna kan lamurra da dama da suka shafi siyasar kasa da kasa tare da sakataren harkokin wajen Amurka, amma suna da sabani a kan mafi yawansu.

Daga cikin muhimman abubuwan da kasashen biyu suke da bababn sabani a kansa kuwa, har batun kasar Venezuela, Syria, da kuma yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya, inda Lavrov ya ce dole ne a warware rikicin Syria ta hanyar lumana, haka ma rikcin da aka haddasa a Venezuela, kamar yadda kuma ya bayyana ficewar Amurka daga yarjejeniyar shirin Iran an nukiliya da cewa babban kure ne gwamnatin Amurka ta tafka.

 

3811679

 

captcha