IQNA

Turkiya Ta Raba Taimakon Abinci Ga Mabukata A Gambia

23:58 - May 25, 2019
Lambar Labari: 3483674
Bangaren kasa da kasa, kungiyar jin kai ta kasar Turkiya ta raba abinci ga mabkata a kasar Gambia domin taimaka musu a cikin watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumar rdaiyo da talabijin ta kasar Turkiya ta bayar ad rahton cewa, a jiya kungiyar jin kai ta kasar Turkiya TIKA ta raba abinci ga mabkata a kasar Gambia.

Isama'ila Safa Yugar jakadan kasar Turkiya a kasar Gambia ya harci wurin raba taimakon, wanda ya kai ton 8 na abinci, inda ya bayyana cewa kasarsa tana gudaar da irin wannan aiki a kasar Gambia tsawon shekaru masu yawa.

Imam Sharif Malik Badjan babban malamin addinin muslunci a kasar wanda shi ma ya halarci wurin, ya bayyana taimakon na Turkiya da cewa abin yabawa ne, musamman ganin cewa akwai mutane da dama masu azumi da suke bukatar irin wannan taimako a kasar.

Kafin wannan lokacin ma wannan cibiya ta kasar Turkiya, ta raba taimakon kayan abinci da wasu kayayykin bukata a gidajen kason kasar Gambia, kamar yadda ta bayar da wani taimakon ga marassa lafiya da suke kwancea  asibitocin kasar.

3814547

 

 

captcha