IQNA

Hukuncin Kisa A Kan Mutane 17 Bisa Laifin Tayar da Bama-Bamai A Masar

14:57 - May 30, 2019
Lambar Labari: 3483688
Kotun daukaka kara a Masar ta amince da hukuncin kisa a kan mutane 17, da kuma daurin rai da rai a kan wasu 19 kan harin majami’a.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya kotun daukaka kara ta Masar ta amince da hukuncin kisa da wata kotu ta yanke a kan mutane 17, da kuma daurin rai da rai a kan wasu mutane 19, wadanda suke da hannu a hare-haren da aka kaddamar da majami’oin mabiya addinin kirista a kasar.

Wadannan mutane dai suna da hannu a hare-hare a kan majami’oi a biranan Tanta, Iskandariyya da kuma yankin Al-abbasiyya a cikin tsakanin shekarun 2016 zuwa 2017.

Harin yankin Abbasiyya da cikin watan Disamban 2016 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 29, sai kuma harin tanta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 27 a ranar 9 ga watan Afirilun 2017, wanda ya zo lokaci guda da harin Iskandariyya, wanda shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18.

 

 

3815375

 

 

 

 

captcha