IQNA

Musawi: Manufar Isra'ila Ita Ce shagaltar Da Musulmi Da Kansu

23:55 - May 31, 2019
Lambar Labari: 3483690
Bangaren siyasa, Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani mai zafi kan masarautar Al Saud dangane da zargin da sarkin masarautar ya yi wa Iran na cewa tana da hannua harin Fujaira.

Kamfanin dillancin labran iqna, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yau Juma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musawi ya bayyana cewa, a kowane lokaci masarautar Al Saud tana hankoron ganin ta aiwatar da abin da iyayen gidanta Amurkawa suke bukata sau da kafa.

Ya ce Iran kasa mai ‘yanci ba za ta taba zama ‘yar koren wata kasa ba, a kan haka dole ne mahukuntan masarautar Al Saud su fahimci haka, kuma kada kugen yaki da neman goyon bayan kasashe domin yakar Iran ba zai yi amfani ba, domin kuwa Iran tana da kyakkyawar alaka da sauran kasashen duniya, kuma ta dogara da kanta ne ba da kasashen turai ba.

Ya kara da cewa abin ban takaici ne yadda Saudiyya za ta kirayi taron gagagwa na kasashen musulmi da sunan kada kugen yaki a  kan Iran, a  daidai lokacin da bata taba kiran wani taron gaggawa kan kisan kiyashin da Isra’ila take yi kan al’ummar musulmi na Falastine ba.

Musawi ya ce kowa ya san kasar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci da sunan addini a  duniya, kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tsaurarn ra’ayi na kisan bil adama da suna jihadi, da suka addabi duniya.

A kan haka ya ce yin tunani da hankali na wann n zamani ba irin na zamanin jahiliyyar larabawa ba, shi ne zai iya kawo sulhu da daidaito a cikin lamurra a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa barazanar Amurka ba ta iya tsorata Iran ba, balanata barazanar masu yi mata ‘yan amashinta.

3815954

 

captcha