IQNA

Malaman Palestine Sun Yi Kira Da A Kaurace Wa Taron Manama

23:58 - June 13, 2019
Lambar Labari: 3483735
Bangaren kasa da kasa, kwamitin malaman Palestine ya bayyana zaman Manama a matsayin wani yunkuri na share sunan Palestine.

Kamfanin dillancin labaran Iqna,  kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya kwamitin malaman Palestine ya gudanar da zama a yankin gaza, inda ya fitar da bayani da ke cewa, babbar manufar taron da ake shirin yi a Mana Bahrain, ita ce share sunan Palestine daga taswirar duniya.

Marwan Abu Ra’as shugaban kwamitin malaman Palestine ya fadia  cikin bayanin bayan taron cewa, suna yin Allawadai da kakkausar murya dangane da wannan taro da Amurka da Isar’ila da kuma wasu daga cikin ‘yan korensu suka shirya.

Ya ce suna son ganin bayan Palestine ko ta wace hanya, bayan kwashe tsawon shekaru wajen saba’in da mamaye musu kasa, ba a iya raba su da kasarsu ta hanyar kisan kiyashin da ake yi musu ba, amma yanzu ana son raba su da kasarsu ta hanyar hada kai tsakanin yahudawa da ‘yanuwansu larabawa.

Bayanin ya kirayi sauran kasashen larabawa masu sauran lamiri da yancin siyasa da su kaurace wa taron, wanda yake a matsayin hainci ga al’ummar Palestine da ma musulmi baki daya.

Amurka da Isra’ila gami da Saudiyya da hadaddiyar larabawa ne dai suka shirya taron mai taken yarjejeniyar karni, da nufin tabbtar da halscin samuwar Isra’ila , da kuma kawo karshen batun kafa kasar palastine mai cin gishin kanta, a maimakon haka za a samarwa falastinawa ayyukan yi karkashin mulkin Isra’ila.

 

3819037

 

 

captcha