IQNA

An Gudanar Da Taro Mai Taken Mahangar Musulunci Senegal

23:52 - July 06, 2019
Lambar Labari: 3483811
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro na kasa da kasa a birnin Dakar na kasar Senegal dangane da mahangar musulunci a kan lamurra zamantakewar dan adam.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin Arab News cewa, a  jiya an gudanar da zaman taro na kasa da kasa a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal dangane da mahangar musulunci a kan lamurra da dama da suka shafi zamantakewa da ma siyasa.

Wanann taro dai ya samu halartar wakilai na cibiyoyin addini daga kasashen duniya daban-daban, inda aka gabatar da kasidu da ke bayyana mahangar muslucni a kan yadda ya kamata zamantakewa ta kasance tsakanin ‘yan baki daya.

Dukkanin mahalarta taron da suka gabatar da jawabai, sun yi ishara da matsalolin da aka haifar a cikin addini sakamakon yaduwar gurbatattun akidu, musamman wadanda suke haifar da ta’addanci da sunan addini, saboda rashin sanin hakikanin addinin musulunci, wanda yake a matsayin addini da ke kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin bil adama.

 

 

3824771

 

 

 

captcha