Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar kasashen musulmin ta OIC ta fitar, ta bayyana cewa dole a dauki matakan gaggawa domin takawa Isra’ila brki dangane da irin take-takenta.
Kungiyar ta ce a cikin wannan makon mai kamawa za ta gudanar da zaman taro tare da halartar wakilan dukkanin kasashen musulmi, domin tattauna halin da ake ciki a Palestine, kan irin matakan da Isra’ila take dauka na mamaye wasu yankunan falastinawa a gabashin birnin Quds, .
Baya ga haka kuma taron na OIC zai dubi kan shirin Isra’ila wanda ta fara aiwatarwa, na gina manyan ramuka a karkashin masalalcin Quds mai alfarama, wanda hakan zai iya yin sanadiyyar ruftawar masallacina kowane lokaci.
Tun daga cikin shekara ta 1967 ce Isra’ila ta mamaye yankunan falastinawa a cikin birnin Quds, kuma take ci gaba da kara fadada mayar yankuann a kowane lokaci.