Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Arabi 21 ya bayar da rahoton cewa,a jiya jami’an tsaron kasar Masar sun kai samamea wata cibiyar muslucni da ke garin Mait Suhail da ke cikin gundumar Minyal Kamh, a cikin lardin Sahrqiyyah.
Wannan farmaki ya zo ne bisa zargin cewa wanann cibiya tana da alaka da wasu bangarorin ‘yan ta’adda, inda aka kae wasu mata uku da aka samua wurin, wadanda aka sake su daga bisani.
Jami’an tsaron kasar ta Masar sun ce wannan na daga cikin irin matakan da suke dauka na yaki da ta’addanci a kasar.
Abin tuni dai a cikin wannan cibiya an gudanar da janazar mamaci ga tsohon shugaban kasar masar Muhammad Morsi, wanda ya rasua lokacin da aka gabatar da shia kotu a kwanakin baya a kasar ta Masar.