Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Watan ya bayar da rahoton cewa, jakadan falastinu a majalisar dinkin duniya Rayadul Maliki ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Nicaragua na da niyyar bude ofishin jakadancinta a Palestine.
Ya ce jami’an diflomasiyyar kasar ta Nicaragua sun sanar da shi cewa, suna cikin shirin bude ofishin jakadanci a birnin Ramallah nan ba da jimawa ba, kuma za su ci gaba da tuntubar juna domin kammala dukkanin shirin da ya kamata kan hakan.
Wannan mataki na Nicaragua na zuwa a matsayin wani martani ga matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin quds, da nufin muzgunawa falastinawa da kuma kwace hakkinsu na mallakar brnin.