IQNA

Sakon Rauhani Na Taya Shugabannin Musulmi Murnar Sallah

23:17 - August 12, 2019
Lambar Labari: 3483938
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murnar sallar idin layya zuwa ga shugabannin kasashen musulmi na duniya.

Kamfanin dillancin labarann iqna, shafin yada labarai na shugaba Rauhani ya bayar da rahoton cewa, shugaba Rauhani ya aike da sakonni daban-daban zuwa ga takwarorinsa na kasashen musulmi, inda yake taya murnar idin babbar sallah.

A cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, yana mika sakon taya murna ga shugabannin kasashen musulmi da sauran al’ummomin musulmi na duniya, tare da yin fatan Allah ya maimaiata mana shekaru masu zuwa a cikin alhairi da kwanciyar hankali da zaman lafiya da ci gaba ga dukkanin al’ummar musulmi, da sauran al’ummomin duniya baki daya.

Rauhani ya kara da cewa, manufar idin layya ita ce sadaukarwa da kuma mika wuya ga umarnin Allah, wanda kuma al’ummar musulmi na bukatar yin koyi da darussan da ke cikin wannan idi mai albarka, domin samun rabo na duniya da lahira.

 

3834355

 

 

captcha