Kamfanin dillacin labaran iqna ya nakalto daga shafin al’ahad cewa, jagoran harkar musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun isa Najeriya bayan da su ka baro India da su ka je neman magani.
Rahotannin da suke fitowa daga Najeriya sun ambaci cewa; Bayan saukarsu a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, jami’an tsaro na farin kaya DSS sun yi awon gaba da su zuwa inda ake tsare da su gabanin tafiyarsu.
Shugaban Harkar musuluncin ta Najeriya, ya isa Najeriya ne a jirgin Ethiopia wanda ya sauka da misalin karfe sha biyu na rana.
A lokacin da yake kasar ta India, shehun malamin ya yi koken cewa ana tsakura masa ta hanyar tsaro mai tsanani da kuma rashin samun likitocin da ya aminta da su.
A ranar Litinin din da ta wuce ne dai Sheikh Ibrahim Zakzaky ya isa kasar India bisa hutun neman magani da wata Kotu a jahar Kaduna ta ba shi.