IQNA

Za A Kai Batun Kashmir Zuwa Kotun Duniya

23:54 - August 22, 2019
Lambar Labari: 3483976
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da cewa za ta mayar da batun Kashmir zuwa ga babbar kotun duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na jaridar Yeni Shafaq ya abyar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Pakistan Shah Muhammad Quraishi ya bayyana cewa, kasarsa tana shirin mayar da batun Kashmir zuwa ga kotun duniya domin daukar mataki na doka kan batun.

Ya ce wannan mataki na zuwa bayan da gwamnatin kasar India ta sanya kafa ta yi fatali da abin da yake rubuce ne a cikin dokoki na kasa da kasa, wanda kuma kotun duniya ce kawai za ta iya yin hukunci a kan wanna batu.

Gwamnatin kasar India ta dauki matakin yin watsi da doka mai lamba 370 da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, wadda ta babbatar da cin gishin kai ga yankin Kashmir, in banda batun tsaro da kuma harkokin waje, amma gwamnatin India ta soke wannan doka.

Daukar wannan mataki dai ya kawo tayar da jijiyoyin wuya a tasakanin kasashen India da kuma Pakistan, inda kwamitin tsaron majalisar majalisar dinkin duniyaya gudaar da zama kan batun, tare da tabbatar da cewa batun Kashmir ba batu ne na cikin gidan kasar India ba, batu ne za a warware shit a hanyar kaidoji na kasa da kasa.

3836465

 

 

 

captcha