IQNA

Lambun Kur'ani A Dubai Daya Daga Cikin Wuraren Bude Ido 100 Na Duniya

23:00 - August 24, 2019
Lambar Labari: 3483981
Bangaren kasa da kasa, mujallar Time ta bayar da rahoton cewa lambun kur'ani na Dubai yana daga cikin wuraren bude ido 100 naduniya a 2019.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, mujallar Time ta bayar da rahoton cewa , bisa binciken da ta gudanar ta kai ga sakamakon cewa, lambun kur'ani na Dubai yana daga cikin wuraren bude ido 100 naduniya a shekarar 2019 da muke ciki.

Rahoton ya ce wannan an gina shi ta hanyar yin amfani da salon fasahar rubutu, inda aka rubuta a yoyin kur'ani da suke yin ishara da wasu abubuwa na musamman.

Daga cikia ai kisoshi wadanda suka zo cikin kur'ani mai tsarki, da kuma yin amfani da fasar rubuta wajen rubuta wasu ayoyi masu jan hanakali.

Baya ga haka kuma an tsara wurin ta yadda zai dauki mutane da yawa, a daidai lokaci guda kuma dukkanin bangarorinsa masu kayatarwa ne da jan hankalin masu bude a wurin.

An yi amfani da fili na hekta 64 wajen gina wurin, kamar yadda a cikin mako da bude wurin, kimanin mutane dubu 100 suka shiga ciki domin dubawa kamar yadda kuma an kashe dirham miliyan 200 domin gina shi.

3836982

 

 

captcha