IQNA

Mutane Daga Kasashe 103 Za Su Halarci Gasar Kur’ani Ta Saudiyya

22:32 - August 26, 2019
Lambar Labari: 3483988
Bangaren kasa da kasa, kasashe dari da uku ne za su halarci gasar kur’ani karo na 41  a birnin Makka kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na alyaum ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin aladu ta sanar da cewa an kammala shirin gudanar da gasar kur’ani ta duniya.

Abdullatif Al Sheikh ministan harkokin yada aladu da addini na Saudiyya ya bayyana, mutane 146 ne za su halarci gasar daga kasashe 103 na duniya kuam za a gudanar da gasar a dukaknin bangarori na harda da tilawa.

Baya ga haka kuma an kasa bangarorin da za a gudanar da gasar, inda kowane bangare yana da alkalai guda 5 kwararru a kan alkalancin gasar kur’ani ta kasa da kasa.

Al sheikh ya kara da cewa, tun daga lokacin da aka fara gudanar da wannan gasa  a karon farkoa  cikin shekara ta 1399 hijira kamariyya ya zuwa yanzu, masu gasa 6300 suka halarci wannan gasa daga kasashen duniya daban-daban.

 

3837585

 

 

 

 

captcha