IQNA

Jordan: Za a Nada Limamai Mahardata Kur'ani Mai tsarki

23:58 - August 27, 2019
Lambar Labari: 3483993
Bangaren kasa da kasa, ministan ma'aikatar harkokin addini na Jordan ya ce za a rika nada mahardata kur'ani a matsayin limamai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Ptra na kasar Jordan cewa, Abdulnasir Abulbasar ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar ya bayyana cewa, daga yanzu idan za a dauki limamai a masallataia  kasar, za a fifita mahardata kur’ania  kan waunsu.

Ya ci gaba da cewa a halin aynzu ma’aikatarsa tana da wani sharia  abnagaren ayyukan kur’ani, inda shirin yake da nufin kara yawan adadin mahardata kur’ani da ake ad su a kasar.

Abdulnasir Abulbasal ya ce, a kowace shekara ana yayae mahardata kur’ani kimanin dubu biyu a kasar, wanda adadin na bukatar  a kara shi.

Dangane da limancin masallatai ya ce, akwai karancin liammai wadana suka hardace kur’ani a kasar.

Saboda haka a nan gaba a cewarsa, limamanci zai zama aikin wadanda suka hardace kur’ani ne koda wani bangarensa ne kamar rabi ko kusa da haka, baya ga sauran ilmomin da ake bukata.

Yahya Saud wakilin makarantar yan mata ta Muhammad Mahmud Saud ya bayyana cewa, suna gudanar da sare-tsarensu cikin nasara, inda suke yaye daruruwan mahardata a kowace shekara.

3837824

 

 

captcha