Kamfanin dillancin labara iqna, jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, wadannan kasashe biyar sun fitar da bayanin nasu ne na hadin gwiwa, domin nuna rashin amincewa da furucin da Netanyahu ya yi, kan cewa idan ya lashe zabe zai hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan da sauran yankunan Isra’ila.
Bayanin ya ce wannan mataki da Netanyahu yake barazanar dauka, zai karo da dukkanin ka’idoji da kuma dokoki na kasa da kasa, a kan haka ba za su taba amincewa da wannan yunkuri ba.
A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana wanna mataki da Netanyahu ke shirin dauka da cewa yana da karya zuciya, kuma ya yi hannun riga da dukkanin dokokin duniya.
A cikin makon da ya gabata ne Firayi minister Isra’ila Bejamin Netanyahu ya fadi a wajen yakin neman zabe cewa, idan ya lashe zaben da za a gudanar a cikin wannan mako, zai hade yankunan Falastinawa na gabar yamma da Kogin Jordan da Isra’ila.
sace