IQNA

Jarabawar Hardar kur'ani mai Tsarki A kasar Kuwait

23:38 - September 15, 2019
Lambar Labari: 3484054
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na jarabawar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar ad wata jarabawa ta hardar kur’ani mai tsarki da kuma tajwidia  kasar Kuwait.

Naser Alkanderi shi ne babban jami’in da ked a wannan shiri a  akarkashin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait.

Ya bayyana cewa wanann shiri yana daga cikin sabbin shirye-shirye da aka fara gudanarwa daga wannan shekara, inda mahardata kur’ani za su rika bayar da jawarabawa da kuma duba tajwidinsu na karatu.

Bayan gudanar da wannan jarabawa mahardatan za su samu sakamako daidaita da yadda suka bayar da jarabawar, kamar  yadda kuma wadanda za su rika wakiltar kasar a tarukan gasar kur’ani a duniya za su zama daga cikin wadanad suka ci jarabawar ne.

 

3842279

 

captcha