IQNA

Netanyahu Ya Kasa Samun Rinjaye A Zabe

20:19 - September 19, 2019
Lambar Labari: 3484065
Bangaren kasa da kasa, manyan jam’iyyu guda biyu Likud da kuma Blue and White suna kusa da juna a zaben Isara'ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, sakamakon farko-farko da hukumar zaben Isra’ila ta fitar ya nuna cewa, manyan jam’iyyu guda biyu Likud da kuma Blue and White suna kusa da juna.

A cikin wani jawabi da ya gabatar ga magoya bayansa a safiyar yau Laraba, firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bai yi da’awar samun nasara ba, kuma an ga alamun damuwa matuka a fuskarsa.

Netanyahu ya ce yanayin da suke ciki na tarihi ne, a lokacin da sakamakon zabe ke tafiya kunnen doki, kumaacewarsa za su fara tattaunawa da abokan kawancensu domin kafa gwamnatin yahudawan sahyuniya mai karfi.

Ya ce suna bukatar gwamnatin yahudawa a Isra’ila mai karfi wadda za ta fuskanci amnyan kalubale da ke a gaban yahudawan Isra’ila, ba gwamnati mai rauni wadda za ta yi kawance da jam’iyyun larabawa ba.

Benjamin Netanyahu ya ce baban kalubalen da ke a gaban Isra’ila a halin yanzu shi ne Iran da kuma kawayenta, wanda suke son ganin bayan Isra’ila.

Sakamakon farko-farko dai ya nuna cewa, jam’iyyar Likud ta Netanyahu tana da kujeru 31 zuwa 33a cikin kujeru 120 a majalisar Knesset, yayin da jam’iyyar adawa ta Blue and white karshin jagorancin tsohon ministan yaki na Isra’ila Benny Gantz take da kujeru 32 zuwa 34.

3843173

 

captcha