IQNA

Rauhani: Ba A Shirye Muke Mu Tattauna Karkashin Matsin Lamba Ba

22:46 - September 27, 2019
Lambar Labari: 3484091
Bangaren siyasa, shugaba Rauhani ya yi watsi da batun tattaunawa karkashin matsin lamba da takunmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya iso birnin Tehran a yau bayan kammala ayyukansa a taron babban zauren majalisar dinin duniya.

Bayan isowarsa irnin Tehran a yau, Dr. Rauhani ya bayyana cewa, ba a cimma matsaya kan abubuwa da dama da Iran ta tattauna da manyan kasashe a kansu ba, amma dai za a ci gaba.

Shugaban na Iran ya ce, bayan isarsa birnin New York wasu daga cikin jami’ai daga wasu manyan kasashe sun yi masa maganar kai harin kan kafanin Aramco na Saudiyya, amma dai babu wanda ya tunkare da batun cewa Iran ce ta kai harin, sai dai wasu sun nuna masa shakku kan cewa mayakan Yemen ba za su iya kai wannan harin ba.

Rauhani ya ce ya ce wasu daga cikin shugabannin kasashe musamman Amurka da wasu ‘yan tsiraru daga cikin turawa da kuma wasu ‘yan koransu daga gabas ta tsakiya, sun fito sun zargi Iran da kai harin na Aramco.

Shugaba Rauhani ya ce ya bukaci kasashen da suke zargin Iran da kai harin da su gabatar da dalilai da suke da su kan hakan, kuma zai koma Tehran yana jiran wata kasa daga cikin kasashen da suke zargin Iran da su aiko masa da dalilai, idan kuma ba haka ba, to zai fi kyau su rufe bakunansu, domin kuwa maganarsu ta zama maganar wofi kenan.

Dangane da batun hankoron da Amurka ta yi ta yi na neman su gana da jami’an Iran awannan taro kuwa, Rauhani ya ce baya da bukatar ya gana shugaban Amurka ko wani jami’in gwamnatin kasar, kuma babu wani batun tattaunawa tsaanin Iran da Amurka a karkashin takunkumi da matsin lamba na siyasa.

3845232

 

 

captcha