IQNA

​UNICEF: Yara Fiye Da Miliyan Biyu Ba Su Karatu A Yemen Saboda Yaki

22:52 - September 27, 2019
Lambar Labari: 3484092
Bangaren kasa da kasa, UNICEF ta ce yakin kawancen Saudiyya kan Yemen ya haramtawa yara fiye da miliyan biyu karatu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumar da ke tallafawa kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da cewa, sama da kananan yara miliyan biyu ne ya haramta wa karatu a kasar Yemen.

A cikin rahoton da hukumar UNICEF ta bayar daga kasar Yemen, ta tabbatar da cewa akwai sama da yara miliyan biyu a halin yanzu da ba su iya zuwa makaranta a kasar Yemen sakamakon yakin da ake kaddamarwa kan kasar.

Rahoton ya ce akwai yara miliyan 3.7 da suke zuwa makaranta amma a cikin zullumi da halin rashin tabbas, domin kuwa a kowane lokaci jiragen yaki na kawancen Saudiyya za su iya yin ruwan bama-bamai a kansu.

Tun kafin wanan lokacin dai hukumar ta UNICEF ta fitar da wasu rahotannin makamantan haka, da suka hada da rahotannin da ke nuni da cewa hare-haren Saudiyya kan al’ummar kasar Yemen sun yi sanadiyyar mutuwar dubban kananan yara tare da jikkatar wasu.

Wasu daga cikin kasashen turai da suke sayawarwa Saudiyya makamai sun dakatar sakamakon kisan mata da kananan yara da ake yi da wadannan makamaiaYemen, yayin da Amurka da Birtaniya kuwa suka kara yawan makaman da suke sayawarwa kasar ta Saudiya, domin ci gaba da yaki akan kasar ta Yemen.

Fiye da shekaru 4 kenen da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen, inda rahoton majalisar dinkin duniya na ranar 17 ga watan Yunin 2019 da aka fara hadawa daga 2016, ya tabbatar da cwa, daga fara yakin ya zuwa yanzu dubban mutane ne suka mutu a bangarori daban-daban na kasar.

 

3844886

 

captcha