IQNA

An Bude Masallaci Mafi Girma  A Yammacin Afrika A Senegal

23:48 - September 28, 2019
Lambar Labari: 3484095
Bangaren kasa da kasa, an bude masallaci mafi girma a yammacin nahiyar Afrika a kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a  jiya Juma’a an bude masallaci mafi girma a yammacin nahiyar Afrika a kasar Senegal tare da halartar dubban mutane.

Wannan masallaci mai suna Masalik Jinan gininsa ya lashe kudade da suka haura euro miliyan 30, wanda akasarin wadanda suka hada wadannan kudade ‘yan darikar Muridiyya ne wadanda suke da rinjaye a yankuna da daman a kasar.

Masallacin dai zai dauki masallata dubu 30, wato dubu 15 a cikinsa, haka nan kuma dubu 15 daga waje, haka ann kuma yana hasumiyoyi guda 5, kowannensu tsawonta ya kai mita 78, kuma an gida masallacin a wurin da fadinsa ya kai hekta 6 baki daya.

3845378

 

 

 

 

 

captcha