IQNA

Dauki Ba Dadi Tsakanin Dakarun Masar Da ‘Yan Ta’adda A Arish

23:58 - September 29, 2019
Lambar Labari: 3484102
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gidan Masar ta ce an kashe ‘yan ta’adda 15 a Arish.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin laaran spunik ya bayar da rahoton cewa, a jiya ma’aikatar harkokin cikin gidan Masar ta bayar da bayanin cewa, an taho mu gama tsakanin jami’an tsaro da kuma wasu gungun ‘yan ta’adda a garin Arish da ke cikin gundumar Sinai ta arewa, kuma an kashe 15 daga cikin ‘yan ta’addan.

Tun a cikin sekara ta 2018 ce da ta gabata dakarun kasar Masar suka fara kaddamar da farmakin neman kawo karshen ‘yan ta’adda a yankin Sinai da ke arewacin kasar Masar, wadanda suke kaddamar da hare-hare da sunan jihadi a kasar.

3845856

 

 

 

 

captcha