IQNA

Jagora: Matsin Lamba Bai Nasara Ba / Za Mu Ci Gaba Matakinn Kan Yarjejeniyar Nukiliya

22:13 - October 02, 2019
Lambar Labari: 3484109
Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da manyan jami’an rundunar kare juyi jagoran juyin juya hali Ayatollah Khamenei ya bayyana matsin da cewa bai yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; A karkashin matsin lamba da takurawa mai tsanani da Amurka take aiki da ita akan Iran, ta kasa cimma manufarta da durkusar da Iran.

Ayatollah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da manyan kwamandojin dakarun kare juyin musuluncin a yau Laraba ya kara da cewa; Amurkawan sun tsammaci ta hanyar yin matsin lamba mai tsanani za su iya tankwara Iran din ta sauya matsayinta na siyasa

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Cikin yardar Allah, yanzu Amurkawan sun fahimci cewa kaikayi ya koma kan mashekiya.

Bayan da Amurkawan su ka tabbatar da babu inda matsin lamabr zai kai su, sai su ka bukaci ganawa da shugaba Hassan Rauhani domin nunawa duniya cewa sun dan sami nasara. Kamar yadda jagoran ya ambata

Wani sashe na jawabin jagoran ya kunshi cewa; Amurkawan sun roki kawayensu turawa da su zama masu shiga tsakani domin haduwa da shugabannin Iran, amma hakan ma ba ta samu ba.

Akan takunkumin da Amurkan ta kakabawa man fetur din Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Matsalar da hakan zai haifar ta dan karamin lokaci ne,amma zai zama mai amfani ga Iran a nan gaba.

3846644

 

 

 

captcha