IQNA

Bunkasa Wuraren Bude Domin Musulmi A Taiwan

22:59 - October 24, 2019
Lambar Labari: 3484187
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Taiwan sun sanar da shirinsu an bunakasa wuraren bude ga musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani ma’aikatar yada labarai a Taiwan ta sanar da cewa, an ware wasu wurare na musammana  birnin Taipei domin musulmi masu bukatar yawon bude ido a kasar.

Bayanin ya ce Taiwan wurae mai ban sha’awa ga musulmi , amma matsalar karancin masallatai, da otel masu abubuwa da musulmi suke bukata da wuraren cin abinci irin na muuslmi, wannan yasa muuslmi basa sha’awar zuwa kasar sosai.

A halin yanzu an samar da wurare kimanin da shida masu kayatarwa da abubuwa wanada musulmi za su bukace su, da kuma masallatai da wuraren ibada da sauran wuraren cin abinci na halal.

Duk da cewa muuslmi suna karanci a Taiwan, amma akwai musulmi da harkokin kasuwanci ke kaisu kasar, kuma suna gudanar da hidimominsu.

Taiwan dai na da cin gishin kai a cikin lamurranta da dama ba tare da dogaro da kasar Sin ba, wanda hakan ya bata damar gudanar da harkokinta da kuma bunkasa tattalin arziki cikin kankanin lokaci.

 

3851963

 

captcha