IQNA

Wace Rawa Saudiyya, Isra’ila, Amurka Suke Takawa A Iraki Yanzu

14:48 - October 31, 2019
Lambar Labari: 3484209
Ga dukkanin alamu haifar da sabon rikici a Iraki sakamako ne na kasa cimma manufar kafa Daesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tun a kwanakin baya ne dai al’ummar kasar Iraki suka fara gudanar da wata zanga-zanga a biranen kudancin kasar da hakan ya hada da birnin Bagadaza, domin yin kira da a kawo karshen cin hanci da rashawa a cikin harkokin gwamnati, da kuma mayar da hankali ga ayyukan gina kasa, da kuma samar wa matasa ayyukan yi.

Da farko dai an fara gudanar da zanga-zangar ne ta hanyar lumana, kuma jama’a ne suke gudanar da ita da kansu ba tare da kutsen wani bangaren siyasa ba a  zahiri, kamar yadda kuma yake rubuce a cikin kundin tsarin mulkin kasar kan cewa, ‘yan kasa suna hakkin su gudanar da jerin gwano na lumana domin gabar da wasu korafe-korafensu ga gwamnati.

Tun a ranakun farko na zanga-zangar kasar ta Iraki, ta fara daukar wani salo wanda ya yi hannun riga da abin da yake a matsayin hakki na masu zanga-zanga bisa tsarin dokokin kasar, inda kafofin yada labarai da daman a kasar sun nuna hotunan mutane dauke da muggan bindigogi a cikin masu zanga-zangar.

Wasu daga cikin hotunan sun nuna wasu suna harbin jami’an tsaro da kuma masu zanga-zangar daga bayan fage, kamar yadda kuma aka rika kai hare-hare a kan kaddarorin gwamnati da dukiyoyin jama’a, inda ake farfasa motocin jama’a tare da kone su, da kuma banka wuta  akan gine-ginen gwamnati da shagunan jama’a, wanda duk wadannan abubuwa ne da suka fitar da wannan zanga-zanagar daga tsari na lumana.

Bayan dakatar da zanga-zangar a lokutan taron arbaeen, an ci gaba da gudanar da ita kasa da mako guda bayan kamala tarukan an arbaeen, wanda kuma har yanzu take ci gaba da gudana, da kuma kara muni.

To sai dai a wannan karo zanga-zangr ta dauki wani salon na daban, inda wasu bangarorin siyasar kasar suka bayyana a matsayin masu tafiyar da ita bisa mahangarsu ta siyasa, da kuma yin amfani da ita domin yin matsin lamba kan gwamnati daidai manufofinsu, tare da karkata akalarta zuwa tashin hankali da ayyukan daba, inda wasu bangaren ‘yan siyasa suke yin amfani da hakan domin gamawa da wadanda suke ganinsu a matsayin abokan hamayyarsu.

Misalin hakan shi ne kone ofisoshin wasu bangarorin siyasa ko kuma na dakarun sa kai na Hashd Sha’abi, har ma da kashe manyan jagororinsu ba tare da wani dalili ba.

Dukkanin wadannan abubuwa ne da masana harkokin siyasar yankin suke ganin cewa ba za su rasa alaka da wani boyayyen shiri da aka riga a ka shirya kan kasar ba, wanda makiyanta suke da hannu a cikinsa kai tsaye.

Musamman ganin yadda kasar ta kama kama hanyar zama ‘yantacciyar kasa, sabanin abin da ‘yan mulkin mallaka suka shirya, inda suka yi zaton cewa bayan kifar da Saddam Hussain, wanda ya kasance babban yaronsu kuma dan korensu da ya yi musu aiki fiye da shekaru 30 a kasar yana kare manufofinsu, bayan da suka gama cin moriyarsa kuma suka gama da shi, ‘yan mulkin mallaka sun zaton cewa za su yi wani sabon mulkin mallaka ne kan kasar Iraki, amma kasar ta kama hanyar zama ‘yantacciyar kasa ta fuskar siyasa da tsaro da tattalin arziki, da kuma yin kawance da kasashen da suke takun saka da ‘yan mulki irin su Iran da sauransu, wannan yasa ‘yan mulkin mallakar suna ganin cewa za su asarar Iraki, kuma suna ganin cewa da a ce kasashe irin su Iran ne suke da tasiria  Iraki, gara a tarwatsa kasar kowa ya rasa, wanda kuma akwai tabbatattun bayanai da aka samu daga wasu daga cikin ofisoshin jakadancin irin wadannan kasashe da ke Iraki da suke tabbatar da wannan shiri, inda masana ke ganin cewa, abin da yake faruwa a kasar Irakia  halin yanzu, alama ce ta fara aiwatar da wanann shiri.

3853605

 

 

captcha