IQNA

An Bukaci Saka Iran A Cikin Tattaunawar Sulhu A Afghanistan

23:55 - November 03, 2019
Lambar Labari: 3484219
Ministan harkokin wajen ya bayyana cewa shigar da Iran a cikin tattaunawar sulhu a Afghanistan na da matukar muhimamnci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Atlas cewa, Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa; a da ake ciki yanzu Rasha da China suna tattaunawa da Amurka da kuma gwamnatin kasar Afghanistan, kamar yadda daga bisani kuma gwamnatin Pakistan ta shiga cikin tattaunawar.

Lavrov ya ce mafi yawan bangarorin wannan tattaunawa suna da ra’ayin cewa ya kama a shigo da Iran a cikin wannan tattaunawa, yin hakan zai taimaka matuka wajen cimma manufar da ake bukata.

Wadannan kasashe dai suna kokarin ganin sun hada jami’an gwamnatin Afghanistan da kuma ‘yan kungiyar Taliban kan teburin tattaunawa domin sulhunta su, amma dai ‘yan kungiyar ta Taliban ne ke kawo ma yunkurin cikas a kowane lokaci.

Ko a kwanakin baya wata tawagar Taliban ta ziyarci Iran, inda aka ba su Magana kan su daure su rungumi suhu da zaman lafiya tsakaninsu da gwamnatin kasarsu, domin a samu zaman lafiya mai dorewaa kasar ta Afghanistan.

3853908

 

 

 

captcha