IQNA

Mata Musulmi 26 Sun Samu Lashe Zaben Majalisun Jihohi A Amurka

23:56 - November 07, 2019
Lambar Labari: 3484233
Bangaren kasa da kasa, majalisar muuslmin Amurka ta sanar da cewa mata musulmi 26 suka samu nasara a zaben majalisun jihohin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labaran IL ya bayar da rahoton cewa, Nahad Awwad shugaban majalisar musulmin kasar Amurka ya bayyana cewa, wannan babban ci gaba ne ga musulmin Amurka, domin hakan shi ne zai ba su damar su kare hakkokinsu a kasar Amurka.

Bisa ga alkalumman da majalisar ta fitar ta bayyana cewa, a cikin shekara ta 2019 musulmi 34 ne suka manyan mukamai a jihohin kasar da suka hada da ‘yan majalisun jihohi daban-daban a Amurka.

Linda Sarsur wata musulma ce ‘yar asalin falastinu a kasar Amurka ta bayyana cewa, sakamakon salon nuna kiyayya ga musulmi da gwamnati mai ci a yanzu ta dauka a kasar Amurka, wannan yasa muuslmi sun mike sun shiga harkokin siyasa a kasar, domin kada a mayar da su saniyar ware.

Ghaleh Hashemi na daya daga cikin musulmin da suka samu nasara a wadannan zabuka a jihar Virginia.

 

3855282

 

 

captcha