Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga mujallar Gulf Today cewa, akalla mutane kiamnin miliyan daya ne suka ziyarci lambun kur’ani a cikin watanni bakawai tun bayan bude shia birnin Dubai na hadaddiyar daular labarawa.
An gina wannan karafaren lambun kur’ani ne a cikin wani fili mai fadin hekta 64, wanda aka gina shi a bangarori 12, kamar yadda kuma aka samar da nau’oin tsirrai 45 da aka ambata a cikin kur’ani.
Haka nan kuma an samar da wasu abubuwa da suke nuni da wasu ababen da aka yi ishara da su a kin kur’ani mai sarki, kamar sandar annabi Musa (AS) da kuma wasu abubuwa na tarihin annabawa da al’ummomin da suka gabata.
Babbar manufar samar da wannan wuri dai ita ce kara jawo hankulan masu yawan bude ido zuwa birnin na Dubai, musamman ma masu son sanin abu dangane da kur’ani.